Dan Sule Lamido na shirin garzaya kotu kan sakamakon zabe
Dan
tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mustapha Sule ya yanke shawarar shiga kotu akan
sakamakon zabe - Lamido dai ya nemi kujerar dan majalisar dattawa mai wakiltan
yankin Jigawa ta tsakiya - Sai dai Lamido ya sha kaye a hannun Sanata Sabo
Nakudu Dan tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma dan takarar kujerar sanata a yankin
Jigawa ta tsakiya a karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP),
Mustapha Sule Lamido ya sanar da shitinsa na kalubalantar sakamakon zaben
majalisar dokoki da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabrairu a kotu.
Mataimakin
Shugaban PDP a yankin Jigawa ta tsakiya, Aminu Jahun ya bayyana hakan ga manema
labarai, cewa za su kalubalanci sakamakon zaben akan zargin magudi da aka tafka
a zaben majalisar dokokin kasa a jihar.
Dan
Sule Lamido ya garzaya kotu kan sakamakon zabe Source: UGC Ku tuna cewa Sanata
Sabo Nakudu ya kayar da dan tsohon gwamnan bayan ya samu kuri’u 224,543 inda
shi kuma dan Lamido ya samu kuri’u 143, 611.
A wani lamari makamancin haka, rahoto a baya
cewa gamayyar kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta zargi
hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da
tursasa mataimakin daraktan kungiyar yakin neman zaben dan takaran shugaban
kasa a jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), da ya mika shaidar da Atiku
Abubakar yake yunkurin yin amfani da su a kotu.
Atiku ya kaddamar da lauyoyi
yan kwanaki da suka gabata don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da
aka gudanar a ranan 23 ga watan Fabrairu inda hukumar INEC ta bayyana dan
takaran shugaban kasa a jam’iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari a
matsayin wanda ya lashe zaben.
0 Response to "Dan Sule Lamido na shirin garzaya kotu kan sakamakon zabe"
Post a Comment