Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku
Kungiyar
masu sarautun gargajiya na kasa (NCTRN) ta shawarci dan takarar shugabancin
kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya amince da sakamakon zaben
shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu. Sarakunan gargajiyan
sunyi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin da suka ziyarci Shugba Muhammadu
Buhari a fadar gwamnati na Aso Rock da ke Abuja.
Tawagar da Sarkin Musulmi,
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III na uku ya jagoranta ta bukaci Shugaba Buhari
ya kasance mai gaskiya da adalci a cikin jagoracin kasar da ya keyi.
Ka
yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku Source: Twitter
Sultan ya tabbatar wa Buhari cewa za su bashi dukkan goyon bayan da ya ke
bukata a yayin mulkinsa na shekaru hudu da zai yi nan gaba.
Ya ce: "Dukkan
'yan Najeriya su amince da sakamakon zaben a matsayin kaddara ta Allah. Allah
ne ya kaddara za kayi tazarce kuma babu wanda zai iya canja hakan. Haka Allah
ya kaddara saboda haka mun ziyarce ka ne domin mu baka goyon baya domin samar
da zaman lafiya da cigaba a kasar mu.
" A bangarensa, Oba Adeyeye Ogunwusi
Ojaja II, Ooni na Ife kuma shima shugaba na kungiyar ya tabbatarwa Buhari cewa
'yan kungiyar za suyi aiki tare da shi domin kawar da miyagun ayyuka a kasar.
Buhari ya roki kungiyar suyi aiki tare da gwamnatinsa domin kawo cigaba a kasa
baki daya.
"Kun san dukkan gidajen da ake boye masu laifi kuma kun san
gidajen da akwai yara na gari. Kune kuka san abubuwan da ke faruwa a lungu da
sako na garuruwa. Muna bukatar goyon bayan ku domin cigaba da ayyukan alheri da
muka fara," inji shi.
0 Response to "Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku"
Post a Comment