Majalisar dokokin Adamawa ta rasa dan majalisa karo na biyu a cikin mako guda
Adamu Kwanate mamba a majalisar dokokin
jihar Adamawa ya mutu - Dan majalisan ya yanke jiki ya fadi ne a lokacin kamfen
- Anyi gaggawan daukar Kwanate zuwa asibitin Yola inda anan ya cika Wani mamba
a majalisar dokokin jihar Adamawa, Adamu Kwanate (APC- Nasarawo/Binyeri) ya
mutu.
Kamfanin dillancin labaran Najeria (NAN) ta tattaro cewa Kwanate a mutu a
ranar Laraba, 6 ga watan Maris kwanaki hudu bayan wani dan majalisa, Abubakar
Abdurahman (ADC-Mubi South) ya mutu bayan yayi fama da dogon rashin lafiya.
Kwanate wanda ke neman tazarce a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris mai zuwa
ya yanke jiki ya fadi a lokacin kamfen a mazabarsa sannan aka yi gaggawan kai
shi asibitin Yolam inda anan ne ya mutu. Mohammed Daji, jami’in bayanai na
majalisar dokokin jihar wanda ya tabbatar da mutuwar dan majalisar yace:
“Yanzun nan na samu mumunan labarin, amma ban rigada na samu cikakken bayanin
abunda ya faru ba." A halin da ake ciki, gaabannin zaben gwamnoni da na
yan majalisar jiha, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga yan Najeriya
inda yayi kira ga su rungumi zaman lafiya a tsarin gudanarwar zaben.
A
jawabin da yayi a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, Shugaban kasar ya bayyana
cewa zabe mai zuwa na da matukar muhimmanci duba ga cewa gwaamnoni da yan
majalisar jiha sun fi kusa da mutane sosai. Shugaba Buhari ya mika ta’aziyya ga
wadanda suka rasa rayukansu ko suka ji rauni da lokacin ayukan ta’addanci da
wasu suka yi yayin zaben Shugaban kasa.
0 Response to "Majalisar dokokin Adamawa ta rasa dan majalisa karo na biyu a cikin mako guda "
Post a Comment