Dalilin Da Kotu Ta Bayar Na Umarnin Kamo Hadiza Gabon
A ranar Alhamis ne wata wata kotun Majistare dake Kano karkashin Alkali Muntari Gambo ta bayar da umurnin a kamo fitaciyyar jarumar Kanywood, Hadiza Gabon saboda rashin amsa gayyatar kotu.
Jarumi a Kannywood Mustapha Naburaska ne ya shigar da kara a kotu kan zargin cin zarafinsa da barazana da ya ce, Jaruma Hadiza Gabon din ta yi masa. An ruwaito cewa Naburaska ya shigar da kara a kotu ne kai tsaye saboda yana fargabar ‘yan sanda ba za su dauki mataki a kan ta ba. Bayan nazarin hujjojin mai shigar da kara, alkalin kotun ya bayar da umarnin a kamo Hadiza Gabon cikin awanni 24 don ta masa tuhumar da ake yi mata tare da kare kanta.
“Ka san cewa Hadiza Gabon tayi suna kuma tana da abokai musamman cikin ‘yan sanda da manyan ‘yan siyasa,” inji wata majiya daga Kannywood. Alkalin kotun Majistare da ke Muntari Dandago ya umurci kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Muhammad Wakili wanda akafi sani da Singham ya kamo jarumar tunda ya ki amsa gayyatar kotu.
“Tunda wacce aka yi kara ba ta da shirin amsa gayyatar kotu, Ina umurtar kwamishinan ‘yan sanda ya sanya a kamo wacce aka gayyata kotun. “Ina kuma umurtan kwamishinan ‘yan sandan ya gudanar da bincike kan zargin da mai shigar da kara ya yi idan an samu gaskiya ciki sai a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kuliya domin ta fuskanci shari’a.
idan za a iya tunawa Jaruma Hadiza Gabon ta sha fuskantar rikice rikice tsakaninta da abokan sana’arta na kannywood, kwanaki ne sunanta ya fito a akan zargin da ta yi ikirarin cewa, Amina Amal ta yi mata na madigo, abin da ya kai ga ta yi wa Amina Amal dukan kawo wuka har suka kai ga gurfana a gaban kotu.
0 Response to "Dalilin Da Kotu Ta Bayar Na Umarnin Kamo Hadiza Gabon "
Post a Comment