Sabbin Masarautu: Abba Kabir yasuf (Gida Gida) Yayi magana Akaron farko
Mun samu labari cewa Abba Kabir Yusuf ya fito yayi magana jiya 22 ga Watan Mayun 2019, a kan kacaccala Masarautun kasar Kano da gwamnatin jihar tayi a kwanan nan. Wannan ne karon farko da 'dan takarar na PDP yayi magana.
Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamna mai-ci Abdullahi Umar Ganduje ya saki layi wajen nada sababbin Sarakuna da yayi a jihar Kano da kuma sallamar Sakatarorin din-din-din daga aiki da kuma sukar Malaman addini.
‘Dan takarar gwamnan na PDP a zaben da ya gabata ya bayyana cewa wadannan matakai da gwamnatin Kano ta ke dauka ba shi ne abin da al’umma su ke bukata a yanzu ba. Yusuf ya bayyana wannan ne wajen wani taron buda-baki.
‘Dan takarar yake cewa sun samu labari cewa za a kashe daruruwan miliyoyi wajen gina fadar Sarakunan da kuma sayewa Sarakunan da ya nada motoci na kasaita a daidai lokacin da ake fama da mutane su na neman abinci da matsuguni.
Haka zalika a jawabin da ‘dan takarar yayi, yace Kano na fama da yara fiye da miliyan 3 da ba su zuwa makarantar boko da kuma matasa miliyan 4 da ba su da abin yi da tarin Almajirai, amma Ganduje ya dage da kirkirar wasu Sarakuna 5 a jihar..
Yusuf ta bakin Sanusi Bature Dawakin/Tofa ya bayyana cewa ba za su yarda da abin da zai raba kan jama’ar Kano da tarihi ba inda yayi farin ciki da kotu ta dakatar da shirin gwamnan. A karshe yayi kira ga jama’a su dage da addu’a a wannan Wata.
0 Response to "Sabbin Masarautu: Abba Kabir yasuf (Gida Gida) Yayi magana Akaron farko"
Post a Comment