CANJIN YANAYI 4


DAGA ALK’ALAMIN Y’AR MUTAN JEGA
©MARYAM ADAM
Kwanaki sun ja ba wani CANJIN YANAYI daga zamantakewar gidan, yanda aka saba tafiya hakan ne har yanzu, sai dai ni kaina na rasa gano wane irin yanayi ne yake so agano ya canja, inda nayi bibiya ko zai furta abin in kwashe amma abin ya faskara.
******
Lamar yanda suka yi alk’awari tsakanin Anty Sis da Hafsat kan cewa zasu kaiwa Anty Jidda ziyara hakan ta kama yau suke ta shirye_shirye inda suka kira Anty Jidda suka jaddada mata cewa zasu kawo mata ziyara.
Da Abban Farha aka shiryar da tafiyar saboda shi zai kai su, sai da ya sauke su Farha gidan Hajiyarshi sannan suka ɗauki hanyar Kano daga katsina har suka kai Kano taɗin kishiya suke yi wanda yake saurarensu yana murmushi k’asa_k’asa.
Da murna Anty Jidda ta taryesu tamkar ta haɗiyesu, Anty Jidda ba dai iya tarbon bak’i ba, sai da ta cika masu gabansu taf da kayan tanɗe_tanɗe da lashe_lashe har zuwa kayan abinci, bayan sunci sun k’oshi ne sunyi hamdala sannan suka lula hirar duniya.
Anty Sis ce ta kai dubanta zuwa ga Anty Jidda kana tace’ “Anty na rako k’awata ne domin ta ganki kuma ki bata lakca akan zaman kishi da kuma kishiya kanta”.
Murmushi Anty Jidda tayi tana mai furta’ “kai Anty Sis ni fa ba Malama bace da kika ɗoran wannan nauyi, sai dai kuma mu’amala da mutane yau da gobe yasa mun ɗauki wasu darussa. Amma ke Maman Farha me yasa kike so a taɓo wannan topic (maudu’i) ne?”.
“Ba komai Anty, inaso ne dai nak’ara ilmin yanda zan zauna da tawa abokiyar zama ne cikin aminci babu cuta ko cutarwar”.
“Alhamdulillah Maman Farha, da za’a samu mata ashirin tamkarki da abubuwa sun rage da dama”.
“Da farko dai inaso musan cewa shi kishi halitta ce, kuma kowane ɗan Adam an halittashi da wannan kishin, sai dai na wani yafi na wani ta yanayin hak’urinshi ko kauda kanshi”.
“Wani haɗuwa ta farko dashi zaki iya fahimtar kalar nashi kishi, zaki ga wani duk tsabar kishinshi yana k’ok’arin dannewa, wani kuma nan take zaki fahimci yana kishi kan abu”.
“Akwai kishi na hankali akwai na rashin hankali”.
“Zamu fara da kishi na hankali irin wanda addini ya yarda dashi. Abu na farko shine, in har Allah ya haɗaki da abokiyar zama to ki fara kwantar da hankalinki har ki gama fahimtar wacece ita da kuma halayyarta sai uwa uba yanayin zamantakewarta da Mijin”.
“A wannan ɓangaren in har kin gama fahimtarta to ki bi tako zaman da ita, duk abinda ta yiwa Mijin na kyautatawa to ki ninka irinshi ta hakan zaki samu babban matsayi a gurin maigidan”.
“Kishi na rashin hankali kuwa shine wanda zaki ga Mata da ance za’a yi masu kishiya kiga suna hauka da zage_zage da cin zarafin Mijin wanda har zai kai baya da sauran mutunci a idonta, a tunaninta hakan zai sa ya fasa auren, wannan kuwa ba shine mafita ba saboda shure_shure baya hana mutuwa duk haukanki ba zai saka ya fasa auren ba, a wannan lokacin ma zai k’ara samun k’warin gwuiwar auro wata saboda yana hango kwanciyar hankali gurin Amaryar”.
“Kuma muddin kika yi sake Amarya ta samu labarin kalar haukarda kika yi da za’a aurota to har abada girmanki zai faɗi a idonta kuma raini zai shiga tsakaninku wanda lokacin da kika so ku fahimci juna hakan ba zata yuyuba saboda an baro kyawo tun ranar haihuwa”.
“A lokacinda duk Amarya ta shigo gidan to uwargida itace tubalin zaman lafiya, saboda a nawa tunanin duk kalar masifa ko wani ji da kai da Amarya ta shigo dashi muddin uwargida na kauda kanta to Amarya zata yi ta gama ne cikin k’ank’anin lokaci saboda ance k’arfe ɗaya baya amo”.
“Amma da wuya asamu uwargida masifaffiya duk kauda kan Amarya gida bai tarwatse ba, saboda tun tana kauda kai zata biyewa Uwargidan ne saboda rashin jan girmanta”.
Gwauron numfashi dukansu suka sauke alamar sun gamsu da zancen nata, sannan Anty Sis ta jefo mata tambaya kamar haka’ “to Anty me yasa naji mutane da dama na furta cewa in gida ya gyaru Maigida ne kuma in ya ɓaci shi ne?”.
Murmushi Anty Jidda ta yi kana ta kurɓi lemun da ke gabansu ajiye ta ɗora da cewa’ “in kinga hakan an samu munafukin Miji ne”.
Maman Farha ce ta yi saurin karɓewa da cewa’ “Anty kamar ya munafukin Miji?”.
“Eh munafuki kam, shine mai ɗaukar hirar Amarya ya kaima uwargida ko mai ɗaukar ta Uwargidan ya kaima Amarya”.
Ido suka gwalo dukansu tamkar k’wank’walati (marfin mirinda).
“Eh mana kuna mamaki ne da kasantuwar hakan?. To bara kuji akwai Namijin da ke ɓata gidanshi da kanshi, saboda kaiwa ɗaya gulmar ɗaya, kuma hakan na tasiri ne da yanda zai samu mai ɗaukar maganar, da idona naga Matan da ke turkar Mijinsu in yaje ya cewa ɗayar wance tace maki abu kaza, tun suna ɗauka har suka fahimci shi ke haɗa husuma tsakaninsu suka fara turkarshi sannan aka zauna lafiya”.
“Kai Anty amma tir da halayya irin ta waɗannan Mazajen kuma ya rabamu da zamantakewa da irinsu”.
Nan Anty Jidda ta amsa da Ameen.
Kusan a tare suka jefo mata tambayar har suna haɗa baki’ “Anty to meke kawo CANJIN YANAYI in har mutum ya k’aro aure?”.
“Wannan yana faruwa ne saboda zank’in Amaryar kuma tana saman kanshi, in har Uwargida ta ɗauke kanta na kwana biyu zata ga cewa Amaryar ma bata taka matsayinta ba, ku auna da kanku kuga yanda in kuna da sabuwar sutura kuke matsuwa baku sanyata ba, kuma in kuka saka ta ɗin zaku jiku wasu daban tamkar kuna saman iska, to ku auna hakan da Miji ya yi sabon aure, kamar yanda suturar nan zata zo ta zama tsohuwa to haka Amaryar zata koma nan gaba kaɗan, kuma har kizo cikin tsofaffin kayanki ki samu wacce kika fi so akan sabuwar nan da kika yi so”.
“Wani CANJIN YANAYIN kuma in kika duba da kanki zaki fahimci yana da asali, wala allah daga uwargidan ne kp kuma Maigidan na da hujjar yin hakan, a koyaushe dai anaso mutum ya kasance mai kyautata zato da kuma kauda kai kan waɗannan abubuwan kuma ya dage da addu’a da tawadu’u a zuciyarshi, in har ya kasance mai kusanci da ubangiji to bashi ba matsalar rayuwa sai dai jarabta ta ibangiji da yake auna k’arfin imanin bayinshi”.
Su dukansu shuru suka yi suna dogon nazari a ransu, nan Anty Sis ta fitar da waya tana kira kan ta shiga Maman Farha ta karɓe tana mai hararta tace’ “wai me kike shirin yi ne?”.
“Ni fa Daddyn Sultan naso na kira”.
“Akan me zaki kira shi bayan kinsan Abban Farhan na jiranmu gidan abokinshi da mun gama zai zo mu wuce?”.
“Ni fa so nake na gaya mai ya fara neman mata daga yau, saboda na fahimci sai ma kanada ita zaka k’ara tantance matsayinka gurin Maigidan”.
Ba Hafsat ba Anty Jidda kanta sai da ta yi dariya sosai sannan ta furta’ “ki barshi hakan in lokaci yayi kina zaune zai zo maki da batun, kinsan shi aure da haihuwa lokaci ne dasu”.
“Allah Anty yanzu na daina jin tsoron kishiya akan wannan bayanin na ki, ko yau zata shigo bana fargaba da hakan”.
“Dace da ta gari shine fatanmu a koyaushe, don haka kiyi ta addu’a”.
Nan suka k’ara tattaunawa kana suka kira Abban Farha yazo suka wuce kowannensu fuska a sake cikin walwala da nishaɗi, tare da ɗinbin tsarabarsu daga Anty Jidda (Allah yasa Anty Sis kar ki manta dani gurin rabo, _lolx_).
Muje zuwa.✍🏻


SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

Seorang Blogger pemula yang sedang belajar

0 Response to "CANJIN YANAYI 4"

Post a Comment