INA DA BURI Kashi na 2
*INA DA BURI 2 *
FEENAT JAFAR
SDY JEGAL
SDY JEGAL
&
HAFSAT (MMN HANEEP)
2_Idonta yayi jajir don tsabar kukan data sha, shikuwa Najib tsohon saurayin ta dake gefe yana faman aikin lalashin sahibar tasa, ya sauke gwauron numfashi kana ya ce
“Ni yakamata nayi kuka bake ba Deeja, ni banga ta inda Allah ya kuskuroni ba da kika kasa tsayar dani matsayin mijin aurenki.

Ido ta dago tana
dubenshi galala,dan haka sai ya cigaba da fad’in
“Wai shin,ni soyayyar ce ban iya ba kome?
“Wai shin,ni soyayyar ce ban iya ba kome?
Wani mugun kallo ta
sauke masa cike yatsine fuska.
“Ka ga,nifa ban kiraka
don ka zauna kanaimin shirme ba, kabani shawarar yanda zanyi donni gaskiya
bazan yarda ayimin auren dole ba dan wannan baya cikin buri na”.
Tsayuwa ya gyara,
Tsayuwa ya gyara,
“To ni yanzu mezan ce
miki khadeja? Kawai kije kicewa Abba ni ki ke so kinga kin huta da fargabar
Wanda za a aura miki…
Shiru sukai ganin Abba
zai shige kowa ya saukar da kai kasa.
“Abba ina yuni..
“Abba ina yuni..
Dan rissina wa yai
Abban yana binsu da ido.
“Lafiya Najib,ya mutan
gidan?
Har su ka gama gaisawa
Abba na hasaaso wani abu cikin ranshi.
Kai ta dafe tare da fad’in
Kai ta dafe tare da fad’in
“Ya ilahi..
Fatan ta Allah yasa
kar Abba yai wa zancen su na yau fassara,dan haka da sauri ta ce
“Kaga shikenan
jeka inna nutsu zanneme ka,dan yau ba wani aikin da zaka min..
Kai ya kad’a yana mata wani kallo na Allah kai damo ga harawa ta shige ciki.
Kai ya kad’a yana mata wani kallo na Allah kai damo ga harawa ta shige ciki.
Kicibis su ka ci da
Kamal a bakin kofar parlour duk su ka kallo juna rai a had’e.
Kauce wa ya yi da niyar ya bata guri itama ta koma inda ya koma,harara ta maka mishi da zummar sauya gu ya sake yin wajen dan haka a masife ta ce
Kauce wa ya yi da niyar ya bata guri itama ta koma inda ya koma,harara ta maka mishi da zummar sauya gu ya sake yin wajen dan haka a masife ta ce
“Malam ka ban waje na
wuce..
Rai ya had’e ganin
zata raina mishi hankali ya ra6a ta gefe ya wuce tana mishi harara.
****
“Ni fa ina ga yaran nan son juna suke Mamyn su..
“Ni fa ina ga yaran nan son juna suke Mamyn su..
Da mamaki Mamyn ta
kallo Abba.
“Su wa fa?
Murmushi ya yi tare da
gyara zama.
“Najib da Deeja nah..
Ido ta sa mishi,jin ba
wanda ta hasaso ya hasaso ba.
“Najib kuma?
“Najib kuma?
Kai ya jijjiga mata.
“Ina ga na samo
mafita, abu d’aya nake tunani bai da aikin yi ban san da mey zai riken Deeja
ba..
“Ni fa Alhaji ba Najib
ya dace da Deeja ba,kamata ya yi ka had’a Deeja da wanda zai iya seta tunaninta
ya juyata ba wai ita ta juya shi ba.
Ido ya sa mata yadda take bayanin,yasan inda ta dosa tunda an ta6o kishiyarta Deeja.
Ido ya sa mata yadda take bayanin,yasan inda ta dosa tunda an ta6o kishiyarta Deeja.
Dan haka da sauri ya
katseta.
“Ban san mey Deeja ta
tsare miki ba,kullum burinki ki ga yarinyar nan na kuka tamkar ba ke ki ka
haifeta ba.
Baki ta saka tana kallonshi,daga fad’in gaskiyar?
Baki ta saka tana kallonshi,daga fad’in gaskiyar?
Kai ta kad’a tare da
jan bak’inta ta rufe,tasan yanzun tata zatai zafi.
****
Aure kam Abba bai fasa ba,duk wata dabararta ta kare daga Najib har Mariya kawarta ba mai wata shawarar da zata bulla mata.
Aure kam Abba bai fasa ba,duk wata dabararta ta kare daga Najib har Mariya kawarta ba mai wata shawarar da zata bulla mata.
Yau tafi kullum kuka
ganin gobe iyanzu ta zama matar Najib.
Zumbur ta mike tare da fita a d’akinta ta nufi d’akin Abba,tabbas wannan ce damarta ta karshe,in ta bari aka aura mata Najib tasan tai babbar wauta a rayuwa.
Kuka reras ta tasa shi gaba tana yi,dan haka tuni ya rikice ya hau tambayar mey ne ne?

“Abba ni fa ka had’ani
da kowa amma banda Najib…
Harshe ta datse jin ta
kwafsa.
Murmushi Umman tai
tana cigaba da dama furarta.
Kai Abban ya girgiza,
Kai Abban ya girgiza,
“Matuka zan sa6a miki
wannan karan Deeja,dan babu abinda zai sa na warware auren nan tunda har gobe
ne za’a d’aura..
Bori ta hau mishi
harda su shusshura k’afa.
Ya sani da matuka yana ji da ‘yarshi tilo d’aya mace tamkar tsoka daya cikin miya.
Ya sani da matuka yana ji da ‘yarshi tilo d’aya mace tamkar tsoka daya cikin miya.
In har ba so yake
zancen Baba Zubairu ya tabbata ba na tsoron Deeja yake toh kwa dole ya nuna
mata aure ba fashi,dan haka kawai sai ya tashi tare da shige wa band’aki ran
shi na kunar jin kukan nata.
Rarrafo wa tai gaban Mamyn.
Rarrafo wa tai gaban Mamyn.
“Dan Allah Mamy ki
taimake ni kar a ban Najib,ni wallahi nafi karfin Najib,na yarda ni nake korar
samarina amma dan Allah kar a ban Najib..
Baki Mamy ta saka,fatan ta Allah yasa Alhaji yaji wannan batu na Deeja.
Baki Mamy ta saka,fatan ta Allah yasa Alhaji yaji wannan batu na Deeja.
“Na sani ai,ki d’auka
wannan ne sakayyar su gare ki da Allah zai musu,baki fara kuka bama sai in kin
ganki a gidan Najib din.
Kuka kam Deeja tasha
shi,hannu bisa kai ta fio a dakin Abban.
Duk da kallo su ka bita duk su na sauraron ihun nata daga saman Abban.
Duk da kallo su ka bita duk su na sauraron ihun nata daga saman Abban.
Murmushi Kamal ya yi
tare da girgiza kai.
A gaban yayun nata ta
zube.
“Ya Salis dan son ku
da Allah kar ku bari a min auren nan da Najib,wai ni yau Abba ya fatattaka…
Kuka ta sa musu,dan haka masu harararta nayi,masu kunshe dariya nayi.
Kuka ta sa musu,dan haka masu harararta nayi,masu kunshe dariya nayi.
A kaf gidan da wanda
bai san halin Deeja bane,ai a ganin su wannan ne dai-dai tunda dama bata da
abokin shawara sai Najib,dan haka a hankali kowa ya fara zame wa tana binsu da
ido.
Kamal ne kad’ai ya rage wanda yasha mur yana kallonta.
Kamal ne kad’ai ya rage wanda yasha mur yana kallonta.
Harara ta sau mishi
duk da kuka take kamin ta mike tana goge hawaye zata wuce
“Ni kad’ai zan iya
taimakon ki Abba ya janye auren Najib kin san wannan..
Chak! Taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba,ta sani da tabbas matuka Abba yana jin shawarar Kamal.
Chak! Taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba,ta sani da tabbas matuka Abba yana jin shawarar Kamal.
“Ki sauke komai ki
bishi ya taimake ki..
Kai ta kad’a jin
shawarar zuciyarta.
A hankali ta juyo tana
mai goge hawaye.
Ya hakimce a kujerar tamkar wani sarki yana dubenta,wannan ce yasan damarshi ta karshe da lalle Deeja zata shigo hannunshi.
Ya hakimce a kujerar tamkar wani sarki yana dubenta,wannan ce yasan damarshi ta karshe da lalle Deeja zata shigo hannunshi.
Kasa ta zauna tare da
kura mishi ido.
“Toh ka taimake ni..
Kallon tara saura
kwata yai mata.
“Wannan ba ladabin roko bane..
“Wannan ba ladabin roko bane..
Harara ta sau mishi
tana had’e rai,sai dai tuno da shine damarta ta karshe yasa ta mike bisa
gwiwarta tare da yin kalar tausayi da yanayin roko
“Dan Allah ka taimake
ni yaya Kamal..
Murmushin mugunta ya saki tare da jijjiga kai ya mike
Murmushin mugunta ya saki tare da jijjiga kai ya mike
“Ashe kin iya ladabi
yarinya..
Wuce wa yai ba tare da
ya sake kallonta ba saman Abba,cike da takaici ta mike ji take tamkar ta shako
shi ta huta,sai dai dole tai ladabi dan ita zai taimaka.
0 Response to "INA DA BURI Kashi na 2"
Post a Comment