INA DA BURI kashi na 1
INA DA BURI*
1
®NAGARTA WRITER’S
ASSOCIATION.
©{SAFHA}
©{SAFHA}
MARYAM ADAM
FEENAT JAFAR
FEENAT JAFAR
&
HAFSAT ISMA’IL
(MMN HANEEP).
Bismillahirrahmanirrahim
Godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata Ala daya bamu ikon fara rubutu lafiya ina rok’on Allah yasa mu gama lafiya, Ameen.
1_Babbar rigar sa ya sab’e tare da sa hannu ya bankad’e labule idonshi akan uwargidansa wacce suke kira da Mamy. Da d’an jimami ya soma magana

“Kinga mutanen nan ko?
har yanzu shuru ba busu babu dalilin su.
Baki Mamy ta d’an ta6e
“Uhm to ni meye nawa a ciki Alhaji? In dai Khadija ce toh idone nawa in an maimaita irin ta wancan karan..
“Uhm to ni meye nawa a ciki Alhaji? In dai Khadija ce toh idone nawa in an maimaita irin ta wancan karan..
Da sauri ya daga mata
hannu tare da fad’in
“Kar ki mana mugun
fata,tuntuni nake fad’a miki wannan zantutukan naki su suke tasiri akan
Deeja”..
Baki taja ta rufe fuskantar bazai gane inda ta dosa ba.
Baki taja ta rufe fuskantar bazai gane inda ta dosa ba.
“Ka d’ai kirata ka ji
ta bak’inta, dan na tabbatar tasan abinda ta kulla..
Jim yai tare da sawa
Mamyn ido,zancenta da kamshin gaskiya,dan haka wannan karan sai ya kwala kiran
Deejan.
Da nutsuwa ta fito fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna gaban iyayen nata.
Da nutsuwa ta fito fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna gaban iyayen nata.
Abba ne ya gyara zama
tare da fad’in
“Nace ya kukai da shi
Aminun kinji da kyau kuwa yau din za suzo akan maganar auren naku?”.
Kai ta dago tare da d’an sato kallon Mamy dake kallonta sai tai da kai kasa.
Kai ta dago tare da d’an sato kallon Mamy dake kallonta sai tai da kai kasa.
“Abba ni banyi waya
dashi ba tun shekaranjiya, jiya ma naita kiransa kuma bai d’aga ba…
“Hmmm,kuma dai..
Mamyn Abba ya kallo
“Meye na wani hmm? Kinga indai bazaki fadi Alkairi ba to kiyi mana shiru”.
“Meye na wani hmm? Kinga indai bazaki fadi Alkairi ba to kiyi mana shiru”.
Hannu ta aza bisa
bak’inta halamun tai shiru.
Shi kanshi Abban
al’amarin Deeja na bashi ciwan kai,sai dai so ya hana ganin laifinta.
“Ni fa bansan me naiwa Aminu ba shekaranjiya k’alau muka rabu dashi da yamma wallahi Mamy”..
“Ni fa bansan me naiwa Aminu ba shekaranjiya k’alau muka rabu dashi da yamma wallahi Mamy”..
Baki Mamyn ta ta6e
halamun meye nata aciki duk Abban na kallon su.
Chan dai ya ce
“Kinga bani lambarsa nakirashi da kaina, in aka bibiya ma suna hanya gosulo ya tare su”…
“Kinga bani lambarsa nakirashi da kaina, in aka bibiya ma suna hanya gosulo ya tare su”…
Baki Mamyn ta saka
tana duben Abban lokacin da Deejan ke miko mishi waya d’auke da numbern Aminu
bisa screen.
Aminun ya kira,sai dai har ta gama ringin ta katse Aminu bai dauka ba har karo na uku.
Aminun ya kira,sai dai har ta gama ringin ta katse Aminu bai dauka ba har karo na uku.
Cike da mamaki ya
sauke wayar tare da ciro tashi ya hau diban numbern zuwa tashi.
Deejan ya mika wa tata
tare da sanya tashi bisa kunne halamun calling.
Bugu d’aya biyu Aminu ya d’aga wayar wanda ke kwance saman gado ya tasa hotunan Deeja a gaba yana jero mata Allah ya isa tun a daren jiya.
Bugu d’aya biyu Aminu ya d’aga wayar wanda ke kwance saman gado ya tasa hotunan Deeja a gaba yana jero mata Allah ya isa tun a daren jiya.
Sallama yai yi cikin
sassanyar murya,take Abban ya shanye mamakinshi ya amsa sallamar.
Daga can b’angaren Aminu ya gyara zaman wayar a kunnan sa
Daga can b’angaren Aminu ya gyara zaman wayar a kunnan sa
“Wa ke magana?”.
Cike da kunar rai Abba
ya ce
“Isma’il ne Mahaifin
Khadeeja…
Mike wa Aminu ya yi
cike da girmama wa yana gaida shi.
Sassauto wa Abban yai tare da amsawa,
Sassauto wa Abban yai tare da amsawa,
“Dama munji shiru ne
ga jama’a na jira daga chan gurin naku..
Jim Aminun ya yi,bai
isa ya cewa Abba kanshi tsaye ya fasa auren Deeja ba,dan haka sai ya hau
kame-kame
“Um dama Abba cewa nai
a bari na kuma shisshiryawa a tsanake in yaso in Allah ya kaimu wani watan sai
naturo ayi maganar auren ina neman wannan alfarmar Alhaji”.
Jim Abban yai,tuni ranshi har ya fara kuna jin zancen Aminun naso ya mayarshi karamin yaro,dan haka ya ce
Jim Abban yai,tuni ranshi har ya fara kuna jin zancen Aminun naso ya mayarshi karamin yaro,dan haka ya ce
“Shekara biyar tayi
maka?
Kai Aminu ya girgiza
da sauri kamar Abban na kallonshi
“A’a Abba,hak’uri za
ayi akwai shirin da nake yi insha Allahu…
Kit ya kashe wayar ba tare da ya jira zancen Aminun ba rai na tafasa,tabbas yasan karan nan ba laifin Deeja ba ne.
Kit ya kashe wayar ba tare da ya jira zancen Aminun ba rai na tafasa,tabbas yasan karan nan ba laifin Deeja ba ne.
Kallota yai yadda ta
fara waro ido tana kallonshi.
“Ke dama wannan yaron d’an k’ananun mutane ne masu baki biyu baki sanar da niba tun wuri sai da na tara jama’a yanzu?
“Ke dama wannan yaron d’an k’ananun mutane ne masu baki biyu baki sanar da niba tun wuri sai da na tara jama’a yanzu?
Kasa tai da kai, sai
ya kallo Mamy wacce nata ido da kunnuwa.
“Mey zanje na cewa
mutanen nan?
“Tabbas wannan abu
akwai rashin kyauta wa aciki.
“Alhaji.
“Alhaji.
Ido ya sa mata
“Ya fa kamata ka
tuhumi Khadija ko akwai tsiyar da ta shukawa yaron nan,ni nasan Aminu yaron
kirki ne kasan babu yanda za ayi haka kurum yace ya fasa auren nan..
Ido Deeja ta zaro tare da kallo Abban,haka yasa a hassala ya ce
Ido Deeja ta zaro tare da kallo Abban,haka yasa a hassala ya ce
“Mey ki ke nufi kenan?
Kina nufin laifin Khadija ne duk da kinji abinda ya ce?
Kai Mamyn ta girgiza
tare da fad’in
“A’a, ni bance ba,dan
haka Allah ya baku hak’uri..
Fuska Deeja ta marairaice tare da yin narai-narai ido kamar za tayi kuka
Fuska Deeja ta marairaice tare da yin narai-narai ido kamar za tayi kuka
“Abba,wallahi ka yarda
bansan me naiwa Aminu ba shekaran jiya k’alau muka rabu fa…
Harara Mamy ta doka
mata cike da takaici,kan ta kai ga magana Salis ya shigo.
“Abba su Baba Zubairu fa sun k’osa da jira.
“Abba su Baba Zubairu fa sun k’osa da jira.
Ajiyar zuciya Abban ya
sau,nan ya sanarshi abinda ya faru.
“Abba to ajira shin
kamar yanda ya ce d’in ko akwai matsalar data tsai dasu”.
Kai ya hau girgiza wa,
Kai ya hau girgiza wa,
“A watan nan da nai
alkawari a shi zan aurar da Khadeeja bazama takai watannin daya d’iba ba
balle yayi tunanin jiransa ta zauna yi, in alfarmar yake nema meya hanashi ya
nema tun kwanaki sai yau da muka zau…
Hannu Deeja ta aza bisa kai tana kallon Abba ido a ware wanda ke sababin zai bawa Aminu mamaki.
Hannu Deeja ta aza bisa kai tana kallon Abba ido a ware wanda ke sababin zai bawa Aminu mamaki.
Tuni taji gabanta na
fad’uwa ganin a yau tai gudin gara gashi zata tadda zago.
Mamy ta kallo wacce ke
murmushi tana kad’a kai tare da bin su Abban da ido.
Tabbas yau karya ta k’are.
Tabbas yau karya ta k’are.
Sumumu ta mike tana
tafe tana had’a hanya,
“Yaushe za a gane wai
ni Deeja *INA DA BURI* ne?
Da6ar ta zauna bakin
katifar d’akinta hawaye na zuba.
Hannu ta aza bisa kai tare da sakar ihun kuka na tuno da shin wa Abba zai bata?
Hannu ta aza bisa kai tare da sakar ihun kuka na tuno da shin wa Abba zai bata?
Tasan ta kad’e har
ganyenta in har aka bata wanda bashi take da buri ba.
****
Hak’uri Abba ya bawa yayun nashi da sauran y’an uwa had’i da sanar su abinda ya yanke,a take su ka goyi bayan shawarar kan a aurar da Khadija dan huce takaicin Aminu da ‘yan baya.
***
Futowar shi kenan daga d’aki kasancewar asabar ce ba zuwa aiki ya jiyo fad’an Mamyn, ko ba’a fad’a ba yasan itada Khadeeja ne don haka kai tsaye ya nufi cikin parlourn.
Kuka wiwi ya samu tanai a gaban Mamy,da ido ya bita yana mai kallon Mamy da halamun tambaya.

“Ai dama nasan bani da
kaffara Kamal,tabbas Khadija na da hannu gurin rushe duk wani shiri na aurenta
in har ya taso.
“Dan bani da abinda zan iya miki,dan fa duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan kan doka..
“Dan bani da abinda zan iya miki,dan fa duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwan kan doka..
Kai Deejan ta dago ido
jajir tare da maka mishi harara,in har taki jinin wani a gidan,toh Kamal ne,dan
haka cike da kara tusa haushi ya sau mata murmushin mugunta Mamy na kallonsu.
Tashi Mamyn tayi tare da yin hanyar kitchen, cike da keta ya kallota wacce har yanzu hawaye take goge wa kanta kasa.
Tashi Mamyn tayi tare da yin hanyar kitchen, cike da keta ya kallota wacce har yanzu hawaye take goge wa kanta kasa.
“Irin ku ai dama a
auren sadaqa ku ke karewa garin ruwan idon *INA DA BURI*..
Chak kukanta ya tsaya tare da kalloshi ba koh kiftawa.
Chak kukanta ya tsaya tare da kalloshi ba koh kiftawa.
Kai ya d’auke daga
kallonta, dan haka sai tai murmushi irin wanda yau tare da fad’in
“Ban yi kama da matan
da za ai sadaqa dasu ba kasan wannan.
“Sannan duk halina bai kai na mai auren auri saki ba dan haka bazai zama laifi ba in har na ce nima *INA DA BURI*…
“Sannan duk halina bai kai na mai auren auri saki ba dan haka bazai zama laifi ba in har na ce nima *INA DA BURI*…
Da sauri ya
kallota,tabbas yasan magana ta ya6a mishi had’i da gori kamar yadda ta saba in
taso sa shi a bakin ciki.
Yau ma kamar kullum yai tsam tare da kallonta,bai san meye laifin Babanshi zai rika zama makamin da za’a rika dukanshi dashi a kullum ba yana jin haushi..
Yau ma kamar kullum yai tsam tare da kallonta,bai san meye laifin Babanshi zai rika zama makamin da za’a rika dukanshi dashi a kullum ba yana jin haushi..
Duk tsiya yasan
iyaye-iyaye ne,ba kuma a sauya musu suna,dan haka yana jin ciwo in har Deeja ta
ci mishi fuska akansu..
Murmushi ya yi tare da gyad’a mata kai.
Murmushi ya yi tare da gyad’a mata kai.
“Hakane,zan so ya
kasance a ni za a bawa sadakar aurenki Deeja.
Rai ta had’e kamar
yadda yai tsammani da sauri,dan haka sai ya girgiza kai tare da fad’in
“Mai da wukar,dan koh a k’afa aka d’aura min ke bazan iya ja ba,sannan nima *INA DA BURI* bana jin kina daga cikin shi..
Tashi yai ya batta baki sake dan tsabar takaici, da kallo Mamy ta bishi wacce ta fito a kitchen sarai ta ji su har ya fuce.

Deeja ta kallo
wacce ke kumfar bak’in
“Ubangiji ya tsareni ni Deeja,koh a mafarki ba za kaga wannan ranar ba wallahi, mugu kawai mai mugun fata..
“Ubangiji ya tsareni ni Deeja,koh a mafarki ba za kaga wannan ranar ba wallahi, mugu kawai mai mugun fata..
Tashi tai tare da
shiga d’akinta cike da kukan takaici.
Tsam Mamy tai tana tunanin wani abu cike da sarkakiya,kai ta jijjiga tana murmushi dan jin shawarar zuciyarta.
Ku jira mu.
Tsam Mamy tai tana tunanin wani abu cike da sarkakiya,kai ta jijjiga tana murmushi dan jin shawarar zuciyarta.
Ku jira mu.
0 Response to "INA DA BURI kashi na 1"
Post a Comment