Manyan wasan Real a watan Fabrairu
Bayan da Madrid ta doke Alaves 3-0 a gasar La Liga a ranar Lahadi, kungiyar za ta buga manyan wasanni a La Liga da Champions League da kuma Copa del Rey a Fabrairu.
Real Madrid za ta fara ziyarta Barcelona a Copa del Rey wasan farko a ranar Laraba a Camp Nou.
A ranar Asabar ne Real za ta je ta kara da Atletico a wasan hamayya a gasar La Liga karawar mako na 23.
Bayan nan ne Madrid za ta fafata da Ajax a wasan farko a gasar Zakarun Turai ta kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.
Ranar 17 ga watan Fabrairu, Real za ta karbi bakuncin Girona a gasar La Liga karawar mako na 24 da za su yi a Santiago Bernabeu.
Daga nan ne Madrid za ta je Levante domin buga wasan La Liga karawar mako na 25 da za su yi ranar 23 ko kuma 24 ga watan Fabrairu.
Real za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu a Copa del Rey a Santiago Bernabeu da ake sa ran yi tsakanin 26 ko 27 ko kuma 28 ga watan na Fabrairu.
Ga wasannin da Real Madrid za ta yi:
- Barcelona-Real Madrid (Copa del Rey wasan farko)
- Atlético-Real Madrid (La Liga wasan mako na 23)
- Ajax-Real Madrid (Champions League)
- Real Madrid-Girona (La Liga wasan mako na 24)
- Levante-Real Madrid (La Liga wasan mako na 25)
- Real Madrid-Barcelona (copa del Rey wasan mako na biyu)
0 Response to "Manyan wasan Real a watan Fabrairu"
Post a Comment