INA DA BURI Kashi na 12
*INA DA BURI*
MARYAM ADAM.
FEENAT JA’AFAR
&
HAFSA(MAMAN HANIF).
12_Ko da ya iso gurin a cike ya tarar da shi da mutane ‘yan zuwa domin fira wasu dan cika kundunsu da shayi,yayinda wasu ke musu akan ball.
12_Ko da ya iso gurin a cike ya tarar da shi da mutane ‘yan zuwa domin fira wasu dan cika kundunsu da shayi,yayinda wasu ke musu akan ball.
Guri ya samu ya zauna
yana saurarensu,har ya tuno lokacin yana single ba wata matsalar cikin gida
kamar su mai shayi.
Ganin sun d’an ragu ne ya sa ya tambayi mai shayin inda zai je ya siyo d’anwake a yanzu.
Ganin sun d’an ragu ne ya sa ya tambayi mai shayin inda zai je ya siyo d’anwake a yanzu.
Duk ido suka sa mishi
da mamaki,
“Kai zaka ci?
Kai ya girgiza tare da
fad’in
“Mai d’aki na ce..
Dariya sosai su ka
harda kyakyatawa.
“Shi yasa nake jin dad’in gauranci watarana, in banda haka a wannan tsohon daren a ina zaka samo d’an wake?
“Shi yasa nake jin dad’in gauranci watarana, in banda haka a wannan tsohon daren a ina zaka samo d’an wake?
Dariya suka sake sanya
wa,dan haka tuni ya sake kuluwa iya wuya.
“Hadi,mu munyi nan,dan
an kwaso maka aiki..
Hadi dake tattare kaya ya jijjiga kai,
Hadi dake tattare kaya ya jijjiga kai,
“Yanzu Hadi ace kai ne
a matsayin da nake a yanzu mey za kai wa matar ka?
Baki Hadi ya washe
yaji anzo gurin,
“Jirani kai dai na
gama had’a kayan nan.
Kai ya kad’a.
Nan ya had’a duk wani
abin buk’atarshi sannan ya cewa Kamal ya biyoshi.
Yanda kasan rak’umi da akala hakan Kamal ya bishi har suka kai shagonshi.
Yanda kasan rak’umi da akala hakan Kamal ya bishi har suka kai shagonshi.
Bayan ya sauke kayan
sannan ya yiwa Kamal nuni da cewa ya zauna,ba musu ya zauna.
“Wato in ne a matsayinka abokina ka ga nan?..
“Wato in ne a matsayinka abokina ka ga nan?..
Katifa ya nuna mishi
da hannu,dan haka sai ya gyad’a kai.
“Zuwa zanyi na kwanta
a nan,in safiya tai
“Kawai shawara guda
zan baka,kayi kwanciyarka anan,in yaso da safe sai na raka ka inda ake siya ka
siyo mata,in ta tambayi dalili ka ce mata da kaje layi ka samu a cike,shine
kabi sahu sai yanzu yazo k’anka…
Tsam ya yi yana tunanin dabara irinta Hadi wacce shi bai ma yi tunaninta ba,yasan in yai haka toh ba makawa ya toshe wannan bangaren,dan haka ba musu ya yarda.
Tsam ya yi yana tunanin dabara irinta Hadi wacce shi bai ma yi tunaninta ba,yasan in yai haka toh ba makawa ya toshe wannan bangaren,dan haka ba musu ya yarda.
“Kai Hadi na
gode,lalle kasan takan mata.
Dariya ya yi sosai sannan yace
Dariya ya yi sosai sannan yace
“Yo,ai ba banza naki
aure da wuri ba,so nake nai degree a karatun dabiar mata da matsalolin su,ka ga
yanzu ma na samo solution na had’i da wata formulan.
Da sauri ya ce
Da sauri ya ce
“Allah Hadi?
Pillow ya gyara tare
da niyar kwanciya.
“Sosai kuwa,waya gaya
maka cewa duk abinda Mata ke so ake yi masu? Ai inn ka biye musu da hakan zaka
wahala wallahi, don ina mai tabbatar ma watarana har d’anwaken za tace ba zata
iya taunawa ba sai ka tauna ka bata ta had’iye”…
Dariya suka sa harda tafawa,shi dai burinshi wacce ya yi dominta taji jiki,gaba ta gane akwai banbanci.
Dariya suka sa harda tafawa,shi dai burinshi wacce ya yi dominta taji jiki,gaba ta gane akwai banbanci.
Hakan kawai yaji
shawarar mai shayi ta kwanta mashi a rai, nan ya biye mai suka yi kwanciyarsu.
****
6angaren Deeja kuwa tana ganin cewa har k’arfe 11:00am ba Kamal ba labarinshi hankalinta gaba d’aya ya soma tashi,sai sintiri take yi daga falo zuwa d’an tsakar gidan.
Bata k’ara tsurewa ba sai da taga agogo ya nuna k’arfe 12:00am, nan ta janyo wayarta ta kira wayar Kamal wacce ranar ya kira ta da ita hankalinta a tashe.
K’arar wayar data jiyo d’aki ne ya yi dai-dai da sakin wani nadamammen kuka nata, yi take yi babu k’akk’autawa, duk inda hankalinta yake a tashe yake, ji take yi tamkar ta fita nemanshi.

Tayi da na sanin
wannan karyar cikin gashi ta jawo Kamal ya 6ace.
Kukan da take yi,iyakar iyarta,chan ‘yan gida suka fad’o mata,dan haka da sauri ta hau kira.
Kukan da take yi,iyakar iyarta,chan ‘yan gida suka fad’o mata,dan haka da sauri ta hau kira.
Kashe wa tai da sauri
dan tuno da mey zata ce toh in an tambayeta?
A tsohon dare ta sashi fitar dole ya siyo d’an wake koh mey?
A tsohon dare ta sashi fitar dole ya siyo d’an wake koh mey?
Kuka sosai take,bazata
iya ba,tuni kanta ya fara sara mata, sai dai ita ba wannan ce damuwarta
ba, damuwarta d’aya taga ta ina Kamal zai 6ullomata, nashe-nashe kawai take yi
a ranta inda abin ya fi tsaya mata a Kamal ya rasu, nan ta sake tsallara kuka
tamkar zata tsage mak’oshinta.
Ranar bacci sai 6arawo,bata san lokacinda ya yi awon gaba da ita ba. Kiran sallah ne ya tayarda ita sai wani jiri take gani kanta na mugun sara mata.
Ranar bacci sai 6arawo,bata san lokacinda ya yi awon gaba da ita ba. Kiran sallah ne ya tayarda ita sai wani jiri take gani kanta na mugun sara mata.
Dube ta fara ganin a
parlour ma tai kwanan zulumi.
Hawaye ne ya zubo mata ganin kofar a garkame halamun bai shigo ba.
Hawaye ne ya zubo mata ganin kofar a garkame halamun bai shigo ba.
Hannu ta aza bisa kai
tare da furta
“Wayyo ni Deeja.
Sai ta sake dasa sabon
kuka,ranar har period d’in dole ne yazo da asubar.
Gari nayin sha ta fito dube Kamal kam wayam har karfe takwas.
Gari nayin sha ta fito dube Kamal kam wayam har karfe takwas.
Gida ta koma tana ta
kwata kiran gida amma ta kasa da sauri tana ta katse kiran.
In ka ganta abin
tausayi idon nan yai luhu-luhu.
Shin wannan din nadama
ce Deeja? Koh kuwa Kauna ce?
SAFHA….
0 Response to "INA DA BURI Kashi na 12"
Post a Comment