Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu
Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu
A fadin
Jarumar, “Ba na son Auren mai kudi ko kadan, kuma kazalika ba na son auren
talaka”
Jamila Umar Nagudu, shaharariyar
‘yar wasan fim na Kannywood ta bayyana wannan ne a wata zaman ganawa da ta yi
da gidan telebijin ‘Kannyflix Programme’ a
wajen shirin su na ‘Mujallar Tauraruwa’
An haifi Jamila ne a ranar 10 ga
Watan Agusta, ko da shike babu tabbacin shekarar da aka haife ta, amma Jamila
ta kasance jaruma ce da kuma masoyanta ke murna da ita sosai ga irin kwarewanta
a fagen wasan kwaikwayo.
Ganin Jarumar ta isa ta yi aure,
kuma kamar yadda ta ke da kyan ganin, za ka iya ransuwa da cewa wata mai girman
kai ce ko kuma watakila macce ce mai son kudi sosai.
Amma abin mamaki shine Jamila ta ce
“Ba na son auren mai kudi, kuma kazala ba na iya auren talaka, saboda shi mai
kudi ba zai ba ni kulawa ta gaske ba ganin irin yada zai yita tafiye-tafiye da
fita iri-iri, kuma ba zai iya zuba ma ni soyayya iri da na ke so ba. lokaci zai
zama masa kadan wajen kulawa da ni” in ji Jamila.
“Ina son ne in auri mutum wanda zai
nuna mani kulawa ta gaske kuma wanda zai biya bukata ta, kuma ya bani lokacin
sa” in ji ta.
Jin hakan zaka iya bayyana irin
macce da Jamila Nagudu ta ke.
A baya, shekara da ta wuce Jamila a
bayanin ta da gidan labaran BBC ta ce “Ibada ne da Shirin fim ne abu mafi muhimanci
a waje na” in ji ta.
Certain dissertation web sites over the internet courses currently have evidently unveiled while in the web-site. BA Result 2019
ReplyDeleteI surprised with analysis research you focused on this into particular put up amazing. Excellent procedure. Thanks...
ReplyDelete2ND YEAR EXAM RESULT
BA 1ST YEAR RESULT
BA 1ST YEAR RESULT
BA RESULT
BA 2ND YEAR RESULT
BA 3RD YEAR RESULT
BA FINAL YEAR RESULT